Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - firaministan Habashar Abiy Ahmed, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa ‘’ wannan babban labari ne ga nahiyar, dama kasashen da zamu iya yin aiki tare dasu’’
Kogin dai wanda aka kashe wa dala biliyan 4.2 a yammacin yankin Benishangul-Gumuz, ya janyo takaddama tsakanin kasashen Habasha da Masar da Sudan tun bayan fara aikin gina shi a shekarar 2011.
Sudan da Masar na fargabar wannan aikin na iya rage kason ruwan da suke samu na ruwan Nilu, yayin da ita kuwa Habasha ke cewa ta hanyar wannan madatsar ruwan za ta samu ci gaba sosai.
An bayyana cewa madatsar ruwan idan an kammala ta kan iya samar da wutar lantarki sama da megawatt 5,000 wanda zai ninka yawan wutar da kasar ke samu.
342/